Hamilton ya lashe tseren Japan Grand Prix

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lewis Hamilton ya lashe tseren motoci takwas a kakar bana

Matukin motar Mercedes, Lewis Hamilton ya lashe tseren motoci ta Formula 1 ta Japan Grand Prix.

Haka kuma matukin Mercedes, Nico Rosberg shi ne ya yi na biyu, sai kuma Sebastian Vettel matukin motar Ferrari ya kammala a mataki na uku a gasar.

Matukin motar Ferrari Kimi Raikkonen ya yi kan-kan-kan a matsayi na hudu a tseren tare da Williams Valtteri Bottas.

Hamilton wanda ya lashe gasa takwas daga guda 14 da ya yi, ya hada maki 48 a matsayi na daya a tseren motoci a duniya, kuma saura gasa biyar da za a karasa a kakar bana.