Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Real Madrid tana mataki na uk a kan teburin La Ligar Spaniya da maki 14

Cristiano Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba a karawar da Real Madrid ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Malaga a gasar La Liga ranar Asabar.

Ronaldo na bukatar cin kwallaye uku domin dara Raul wanda ya ci wa Real Madrid kwallaye 323 a matsayin wanda yafi ci mata kwallaye a raga.

Ronaldo shi ne dan wasan Real Madrid dake kan gaba wajen ci mata kwallaye a gasar La Liga, a inda ya zura 230 a raga.

Malaga ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nordin Amrabat jan kati saboda ketar da ya yi wa Marcelo.