An kara wasanni biyar a 2020 Olympics

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birnin Tokyo ne zai karbi bakuncin wasannin Olympics a 2020

An amince a kara wasanni biyar a kan wadanda ake yi a gasar wasannin Olympics da za a yi a 2020 da birnin Tokyo zai karbi bakunci.

Sabbin wasannin da aka amince da su, sun hada da na wasan zamiyar kankara da na ruwa wato Surfing da kwallon baseball da na hawa tsauni da kuma Karate.

Jumulla za a yi wasanni sama da 23 da 'yan wasa sama da 474 za su fafata domin lashe lambobin yabo a gasar.

Kwamitin Olympics na duniya zai zauna taro a cikin watan Agusta domin cimma matsayi a wasannin Olympics din na 2020.

Kimanin wasanni takwas aka zabo daga cikin mambobin kasashe 26, musamman wasannin da za su iya jawo mabiya da dama da kuma samun damar tallata su.