An tuhumi Mascherano da kin biyan haraji

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana tuhumar Mascherano da laifin kin biyan haraji

Hukumar tara kudaden haraji ta Spaniya na tuhumar dan kwallon Barcelona, Javier Mascherano da laifuka biyu kankin biyan haraji.

Hukumar na tuhumar Mascherano dan kasar Argentina da laifin kin biyan haraji da ya kai kudi yuro miliyan daya da rabi.

Ana tuhumar dan wasan da boye kadararsa da yake samu ta wajen tallace-tallace ta kamfanin da ya kafa a Amurka da Portugal.

Kotun kasar Spaniya ce za ta bayar da izini idan ya dace a fara sauraren tuhumar ko kuma akasin hakan.

Mascherano mai shekaru 31, ya koma Barcelona da taka leda daga Liverpool a Agustan 2010 kan kudi £17.25m.

A shekarar 2011 an zargi dan wasan da kin biyan haraji da ya kai kudi £434,681 da kuma £716,485.74 a 2012.