Da kyar mu maye gurbin Messi a Barca - Enrique

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Enrique ya ce da kyar ne idan za su iya maye gurbin Messi a Barcelona

Da wuya mu maye gurbin Lionel Messi a Bracelona in ji koci Luis Enrique, a shirin da suke na karawa da Bayer Leverkusen a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Messi mai shekaru 28, zai yi jinyar makonni bakwai zuwa takwas, bayan da ya ji rauni a wasan da Barcelona ta ci Las Palmas 2-1 a gasar La Liga ranar Asabar.

Enrique ya ce "Kalubale na a garemu da muka rasa fitatcen dan kwallon kafa na duniya sakamakon raunin da ya ji".

Messi ya ci kwallaye 43 a gasar La Liga a kakar bara da kuma zura kwallaye 10 a raga da suka taimaka wa Barcelona lashe kofin zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 28, ya dara Cristiano Ronaldo na Real Madrid da kwallaye uku a matsayin dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar cin kofin zakarun Turai, a inda ya ci 77.

Messi wanda ya dauki kofin zakarun Turai hudu ba zai buga wa Barcelona wasanni takwas ba, amma zai iya nurmurewa domin karawa a wasa da Real Madrid ranar 22 ga watan Nuwamba.