Bale ya dawo atisaye bayan jinya

Image caption Bale zai iya buga wa Real wasan da za ta yi da Atletico Madrid

Gareth Bale ya dawo atisaye domin buga wa Wales wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za ta yi a cikin watan Oktoba.

Bale ya ji rauni ne a karawar da Real Madrid ta doke Shakhtar Donetsk ranar 16 ga watan Satumba a gasar cin kofin zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 26, bai buga wa Real Madrid wasanni uku ba, sakamakon raunin da ya ji, zai kuma dawo da buga mata tamaula a karawar da za ta yi da Atletico Madrid ranar 4 ga watan Oktoba.

Wales za ta kara da Bosnia-Herzegovina a Zenica ranar Asabar 10 ga watan Oktoba, sannan ta karbi bakuncin Andorra a ranar Talata.