Iyayen Neymar sun kare shi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar na haskakawa a Barcelona

Iyayen dan kwallon Brazil, Neymar sun musanta cewar dansu na da laifi, bayan da wani alkali ya zarge shi da kin biyan haraji na kusan dala miliyan 16.

A cewarsu, alkalin bai fahimci ainihin arzikin dansu ba.

Alkalin ya zargi Neymar da bayyana kashi takwas cikin 100 na dukiyarsa, a shekara ta 2013.

Yanzu haka alkalin ya haramta wa Neymar ta ba dukiyarsa da ta kai fiye da dala miliyan 47.

Neymar ya koma Barcelona ne a watan Yunin 2013, bayan nasarar da ya samu a wasansa a kungiyar Santos ta Brazil.