'Akwai rashin tabbas a halayyar 'yan Chelsea'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea za ta kara da tsohuwar kungiyar Mourinho FC Porto a gasar cin kofin zakarun Turai

Kociyan Chelsea, Jose Mourinho, ya tuhumi wasu 'yan wasansa da nuna halayyar rashin tabbas a lokacin wasanni saboda yadda kulob din ya fara gasar bana da rashin kokari.

Mourinho, wanda ya jagoranci Chelsea ta lashe kofin Premier a bara, amma take mataki na 14 a kan teburin bana ya ce sun rasa karsashin zakaru.

Kociyan ya kara da cewar da zarar 'yan wasa sun fara nuna halayyar rashin tabbas ta fuskar kwarin gwiwa da sadaukarwa a wasanni, dole a samu koma baya a wasannin kulob.

Chelsea ta lashe kofin Premier bara da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City, amma ta kasa lashe wasannin gasar Premier biyar daga bakwan da ta buga a bana.

FC Porto za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata a Portugal.