'Man United za ta iya lashe kofin zakarun Turai'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana mataki na daya a kan teburin Premier bana

Manchester United za ta iya daukar kofin zakarun Turai nan da 2017 in ji kociyanta Louis van Gaal.

Van Gaal mai shekaru 64, shi ne ya maye gurbin David Moyes a 2014, ya kuma jagoranci United ta kammala a mataki na hudu a kan teburin Premier bara.

Rabon da United ta lashe kofin zakarun Turai tun a 2008, ta kuma yi ta biyu sau biyu a 2009 da kuma 2011.

Van Gaal ya ce 'Yana harin kai wa wasan karshe a gasar da kuma fatan samun nasarori da za su ba shi damar daukar kofin'.

Kociyan ya lashe kofin zakarun Turai tare da Ajax a 1995, sannan ya yi na biyu a gasar da Bayern Munich a 2010.

Manchester United za ta fafata da Wolfsburg a wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba a Old Trafford.