An ci kwallaye 663 a raga a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto lmgnfpl twitter
Image caption Enyimba ce ke mataki na daya a kan teburin Firimiyar Nigeria

Bayan da aka buga wasannin mako na 31 a gasar cin kofin firimiyar Nigeria, an zura kwallaye 663 a raga a gasar, bayan da aka buga wasanni 310.

Haka kuma Alkalan gasar sun bai wa 'yan wasa 53 jan kati da kuma raba katin gargadi 1,088 tun lokacin da aka fara wasannin.

Enyimba ce ke matsayi na daya a kan teburi da maki 58, sai Sunshine Stars mai maki 53 a mataki na biyu, yayin da Wikki Tourists ke da maki 51 ta uku a kan teburin.

Kano Pillars mai rike da kofin bara, tana mataki na takwas da maki 45.

Kungiyoyi hudu da ke karshen teburin sun hada da Dolphins wacce take matsayi na 17 sai Kwara United a mataki na 18, FC Taraba ce ta 19 sai kuma Bayelsa United ta 20 a teburin.

Za a ci gaba da buga gasar firimiyar Nigeriar wasannin mako na 32 a ranar 4 ga watan Oktoba.