Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 19 Super Eagles

Image caption Super Eagles za ta buga wasannin sada zumunta da Jamhuriyar Congo da Kamaru

Kociyan tawagar kwallon kafar Nigeria, Sunday Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 19 masu taka leda a gida, domin tunkarar Burkina Faso a Fatakwal.

Oliseh na fatan 'yan wasan da ya gayyato za su halarci sansanin atisaye a ranar 4 ga watan Oktoba, domin buga karawa da Burkina Faso a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Nigeria za ta kara da Burkina Faso a filin wasa na Adokiye Amiesieamaka da ke Fatakwal a ranar 18 ga watan Oktoba, sannan ta ziyarci Ouagadougou a wasa na biyu ranar 25 ga watan Oktoba.

Kafin karawa da Burkina Faso Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Jamhuriyar Congo a ranar 8 ga watan Oktoba, sannan ta fafata da Kamaru kwanaki uku tsakani.

Ga sunayen 'yan wasan da Oliseh ya gayyata:

Masu tsaron raga: David Obiazor (Heartland FC); Okemute Odah (Warri Wolves)

Masu tsaron baya: Kalu Orji (Enugu Rangers); Solomon Kwambe (Warri Wolves); Idris Aloma (Enyimba FC); Samson Gbadebo (Lobi Stars); Jamiu Alimi (Shooting Stars); Stephen Eze (Sunshine Stars)

Masu wasan tsakiya: Abdulrazaq Abdul (Enyimba FC); Ifeanyi Mathew (El-Kanemi Warriors); Usman Mohammed (FC Taraba); Bature Yaro (Nasarawa United); Osas Okoro (Enugu Rangers)

Masu wasan gaba: Ezekiel Bassey (Enyimba FC); Gbolahan Salami (Warri Wolves); Godwin Obaje (Wikki Tourists); Tunde Adeniji (Sunshine Stars); Bright Onyedikachi (FC IfeanyiUbah); Dayo Ojo (Sunshine Stars)