Kompany ba zai buga karawar Man City da Borussia ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vincent Kompany ya ji rauni a kafarsa.

Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany yana cikin 'yan wasan kungiyar guda shida da ba za su buga karawar da za ta yi da Borussia Monchengladbach a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba.

Kompany ya ji rauni a kafarsa, don haka zai bi sahun 'yan wasa Gael Clichy, Fabian Delph, Eliaquim Mangala, Samir Nasri da kuma Wilfried Bony, wadanda su ma za su ci gaba da zama a gefe sakamakon jinyar da suke yi.

Yaya Toure da David Silva sun yi atisaye ranar Talata bayan murmurewar da suka yi.

Kungiyar ta sha kashi a hannun Juventus a wasanta na farko na rukunin D.