Ronaldo ya kamo Raul a Real Madrid

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ronaldo ya gawurta a Real Madrid

Cristiano Ronaldo ya kamo Raul a yawan zura kwallaye a Real Madrid sannan kuma ya zura kwallaye 501 a tarihin kwallonsa.

Dan kwallon ya zura kwallaye biyu a wasan da Real ta doke Malmo a Sweden da ci biyu da nema.

A yanzu Ronaldo ya yi kan-kan-kan da Raul inda kowannensu ya zura kwallaye 323 a rigar Real Madrid.

"In kafa tarihi a Real Madrid abin alfahari ne. Na ji dadin zura kwallo a nan Sweden," in ji Ronaldo.

Sakamakon sauran wasanni a gasar zakarun Turai:

  • Man Utd 2-1 VfL Wolfsburg
  • FC Astana 2-2 Galatasaray
  • Atl Madrid 1-2 Benfica
  • Borussia Mönchengladbach 1-2 Man City
  • Juventus 2-0 Sevilla
  • Malmö FF 0-2 Real Madrid
  • Shakt Donsk 0-3 Paris St G
  • CSKA 3-2 PSV