Sturridge ba zai buga wasu wasanni ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan Liverpool Daniel Sturridge

Kungiyar kwallon kafa ta England ta ki sanya dan wasan gaba na Liverpool Daniel Sturridge a cikin wadanda zasu buga wasanninta da Estonia da Lithuania, na neman shiga gasar kwallon kafar Turai na 2016.

A karon farko, an kira dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli da kuma dan wasan gaba na Liverpool, Danny Ings da su buga wasannin, ganin yadda suka wakilci England a gasar 'yan kasa da shekaru 21.

Sturridge wanda ya dawo daga jinya ya ci kwallaye biyu a karawar da Liverpool ta doke Aston Villa da ci 3-2 ranar Asabar.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce dan wasan ba zai iya buga duk kan wasannin na England ba.

Kazalika, dan wasan Southampton Ryan Bertrand da Phil Jones na Man-U da kuma Adam Lallana na Liverpool wadanda basu samu buga wasannin da England ta yi da San Marino da Switzerland a watan Satumba ba, suna daga cikin wadanda zasu buga wasannin na gaba.

Tuni England ta samu cancantar shiga gasar kwallon kafar Turan wanda za a yi a Faransa.