Sevilla ta ci Barcelona 2-1 a La Liga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona za ta buga da Rayo Vallecano a wasan gaba

Sevilla ta doke Barcelona da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na bakwai da suka fafata a ranar Asabar.

Sevilla ta ci kwallayenta ne ta hannun Krohn-Dehli a minti na bakwai da dawo wa daga hutu, sannan ta kara ta biyu ta hannun Iborra.

Ita kuwa Barcelona ta zare kwallo daya ta hannun Neymar Da Silva wanda ya ci daga bugun fenariti.

Da wannan sakamakon Barcelona tana nan da makinta 15, yayin da Sevilla ta hada maki takwas bayan buga wasanni bakwai.

Sevilla za ta ziyarci SD Eibar a wasan mako na 8, yayin da Barcelona za ta karbi bakuncin Rayo Vallecano.

Za a ci gaba da wasannin cin kofin Spaniyar La Liga a ranar Lahadi:

  • Rayo Vallecano vs Real Betis
  • Athletic de Bilbao vs Valencia C.F
  • Levante vs Villarreal CF
  • Atletico de Madrid vs Real Madrid CF