Arsenal ta zazzaga wa Man United 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier, yayin da United ta koma matsayi na uku

Arsenal ta ci Manchester United 3-0 a gasar Premier wasan mako na takwas da suka kara a Emirates ranar Lahadi.

Arsenal ta fara cin kwallon farko ta hannun Alexis Sanchez a minti na shida da fara wasa, sannan Mesut Ozil ya kara ta biyu dakika 74 tsakani da kwallon farko.

Sanchez ne ya kara cin United kwallo ta uku daga tazarar yadi 18, kuma wannan shi ne karo na biyu da Arsenal ta samu nasara a cikin wasanni 14 da suka buga a tsakaninsu.

Arsenal ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 16, yayin da Manchester United ta dawo matsayi na uku a kan teburin ita ma da maki 16 da bambancin kwallaye tsakaninsu.