Everton da Liverpool sun buga 1-1

Image caption Everton ta hada maki 13, yayin da Liverpool ke da maki 12

Everton ta tashi wasa 1-1 da Liverpool a gasar Premier wasan mako na takwas da suka fafata a Goodison Park ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Danny Ings da kai, daga bugun da James Milner ya yi wo masa.

Romelu Lukaku ne ya farke wa Everton kwallon da aka zura mata, bayan da Emre Can ya buga kwallo ta kuma bugi jikin Martin Skrtel ta fada hannunsa.

Everton za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na tara, yayin da Liverpool za ta ziyarci Tottenham a White Hart Lane.