An tuhumi Mourinho da rashin da'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Jose Mourinho da halin rashin da'a, saboda kalaman da ya yi bayan da Southampton ta ci Chelsea 3-1 a ranar Asabar.

Hukumar ta ce jawaban da kocin ya yi sun nuna cewar alkalan da suka jagoranci karawar a Stamford Bridge ba su yi masa adalci ba.

Mourinho ya zargi alkalin wasa Robert Madley da hana Chelsea fenariti biyu a ranar Asabar din, har ma ya kara da cewa alkalai na fargabar ba su bugun fenariti.

An bai wa Mourinho daga nan zuwa ranar 8 ga watan Oktoba domin ya kare kansa.

Doke Chelsea da Southampton ta yi da ci 3-1 a gasar Premier ya sa Mourinho ya yi rashin nasara a wasanni hudu a bana, yana kuma mataki na 16 a kan teburi.