Chelsea na goyon bayan Mourinho

Image caption Sau hudu Chelase tana yin rashin nasara a gasar Premier ta bana

Chelsea tana goyon bayan Jose Mourinho, duk da kasa yin abin kirki a gasar Premier ta bana, wanda rabon da ta yi hakan tun 1978-79.

A ranar Asabar Southampton ta doke Chelsea da ci 3-1 a Stamford Bridge, wanda hakan ya sa ta koma ta 16 a kan teburin Premier.

Bayan da suka tashi daga karawar ne Mourinho ya sanar da Sky Sports cewar sai dai kungiyar ta sallame shi idan ba ta bukatar aikin da yake yi.

Chelsea ta bayar da sanarwar cewar tana mara wa Jose Mourinho baya dari bisa dari.

Tuni ma kyaftin din kungiyar John Terry ya ce Mourinho ne kadai zai fitar da Chelsea daga halin da ta tsinci kanta a ciki.