'Mu na goyon bayan Mourinho'

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mourinho na tsaka mai wuya

Kungiyar Chelsea ta ce tana goyon bayan kocin tawagar Jose Mourinho, bayan da kungiyar ta soma kakar wasa mafi rashin tabbas tun a shekarar 1978 zuwa 1979.

A ranar Asabar Southampton ta doke Chelsea da ci uku da daya abin da ya bar kungiyar a matakin na 16 a kan tebur.

Bayan rashin nasarar, Mourinho ya shaida wa Sky Sports cewar kungiyar za ta iya korar sa idan ba sa son aiki tare da shi.

"Kungiyar na goyon bayan Jose domin ci gaba da jan ragama," in ji sanarwar kulob din.

"Mun yi ammana shi ne manajan da ya fi dacewa kuma yana da tawagar da za ta taimake shi."