Sunderland za ta dauki David Moyes

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A ranar Lahadi Dick Advocaat ya yi ritaya daga horas da Sunderland

Sunderland na duba yiwuwar dauko kociyan Real Sociedad, David Moyers, a matsayin wanda zai maye gurbin Dick Advocaat.

Advocaat ya yi murabus daga horas da Sunderland a ranar Lahadi, bayan da kungiyar ta tashi wasa 2-2 da West Ham a gasar Premier.

Sunderland wacce take mataki na 19 a kan teburin Premier na neman sabon mai horas da 'yan wasan tamaula da zai jagoranceta.

Kuma kungiyar na fatan nada sabon koci kafin wasan gasar Premier da za ta yi da West Brom a ranar 17 ga watan Oktoba.

Sai dai kuma Sam Allardyce da Nigel Pearson da kuma mai horas da Burnley Sean Dyche na daga cikin wadanda ake ganin za a zaba.

Har yanzu Sunderland ba ta ci wasa ba a gasar Premier da aka yi ta bana.

David Moyes tsohon kociyan Manchester United da Everton ya fara horas da Real Sociedad a watan Nuwambar bara, kuma kungiyar na daga kasa-kasan teburin La Liga Spaniya.