An zabi Bale gwarzon dan kwallon Wales

Image caption Kwallayen da Bale ya ci ne suka taimakawa Wales kai wa daf da samun tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai

Hukumar kwallon kafar Wales ta zabi dan wasan Real Madrid Gareth Bale a matsayin dan kwallon kafa da ya fi yin fice a 2015.

Wannan shi ne karo na biyar da Bale yake lashe kyautar, kuma shi ne fitatcen dan kwallo da 'yan wasa da kuma magoya baya suka ce ya fi haskakawa a banar.

Dan wasan mai shekara 26, ya yi fama da kalubale a shekara ta biyu da ya yi a Real Madrid, bayan da kulob din ya kasa kare kofin zakarun Turai da ya dauka a 2013-14.

Bale ya ci wa Wales kwallaye shida a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a bana.

Haka kuma Wales din na daf da samun tikitin zuwa gasar badi da za a yi a Faransa, wanda rabonta da shiga gasar tun a shekarar 1958.

Wadanda aka karrama maza:

  • Gwarzon dan kwallon kafa: Gareth Bale
  • Dan kwallon da 'yan wasa suka zaba mafi fice: Gareth Bale
  • Dan wasan da magoya baya suka ce ya fi kwazo : Gareth Bale
  • Matashin dan wasa: Tommy O'Sullivan
  • Dan wasan da 'yan jaridu suka zaba: Chris Coleman

Kyautukan da aka bai wa mata:

  • Gwarzuwar 'yar wasa: Kylie Davies
  • 'Yar kwallon da 'yan wasa suka zaba: Helen Ward
  • 'Yar wasan da magoya baya suka zaba: Natasha Harding
  • Matashiyar 'yar wasa: Charlie Estcourt