Spain ta bar tuhumar Messi kan kin biyan haraji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Spain ta ce za ta ci gaba da tuhumar mahaifin Messi kan kaucewa biyan kudaden haraji

Masu shigar da kara a Spaniya sun ajiye tuhumar da suke yi wa Lionel Messi kan kin biyan haraji, amma za su ci gaba da tuhumar mahaifinsa.

Idan har aka samu mahaifin Messi mai suna Jorge da laifi, zai iya zaman jarun na tsawon watanni 18 da kuma biyan tara ta kudi yuro miliyan biyu.

Tun farko masu shigar da karar sun tuhumi Messi da mahaifinsa kan rufa-rufar kin biyan harajin da ya kai kudi sama da yuro miliyan hudu.

Spain ta ce mahaifin Messi ya yi amfani da wasu kamfanoni a Belize da kuma Uruguay daga tsakanin 2007 da kuma 2009 domin boye hakikanin kudaden da dansa ke samu a harkar kwallon kafa.

Lauyoyin Messi sun ce dan kwallon bai ta ba samun lokacin da ya zauna domin nazartar yadda ake juya masa kudaden ba.

A watan Agustan 2013, Messi da mahaifinsa suka biya yuro miliyan biyar dai-dai da kudaden harajin da ake zargin sun ki biya.