Ban aikata ba dai-dai ba a Fifa - Blatter

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter zai sauka daga shugabantar Fifa a watan Janairu

Shugaban hukumar Fifa, Sepp Blatter ya ce yana takaici da ake yin Allah wadai da shi, ba tare da an same shi da laifin aikata ba dai-dai ba a hukumar.

Blatter ya ce Chung Mong-joon wanda yake son gadar kujerar shugabancin Fifa ya taba ce masa munafiki kuma makarya ci, har ma ya yi kokarin gurfanar da shi a gaban kotu kan almubazzaranci a Fifa.

Ana binciken Blatter da kuma tuhumarsa da zargin cin hanci da rashawa tsawon lokacin da ya fara jagorantar Fifa.

Blatter mai shekaru 79, ya shaida wa mujallar Bunte ta Jamus cewa zarginsa kawai ake yi zai kuma kare kansa.

A ranar Labara ce tsohon mataimakin shugaban Fifa, Chung Mong-joon ya ce kwamitin da'a na hukumar na bincikarsa, wanda hakan zagon kasa ne ga takarar kujerar Fifa da yake yi.