Super Eagles za ta kara da Congo da Kamaru

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Nigeria za ta fara wasan sada zumunta da Congo sannan ta fafata da Kamaru a Belgium

Kociyan tawagar kwallon kafa na Super Eagles Sunday Oliseh ya umarci 'yan wasa shida da suka sami matsalar biza a Abuja da su koma sansanin horo na Fatakwal.

Tun farko ofishin jakadancin Belgium ya hana wasu 'yan wasan Nigeria takardar izinin shiga kasar domin buga wasan sada zumunta da za ta yi a can.

Oliseh ya kuma mika goron gayyata ga Kingsley Madu da ke taka leda a AS Trencin ta Slovakia da Wilfred Ndidi da ke wasa a KRC Genk da kuma Dele Alampasu na Club Desportivo, da ke Portugal.

Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Jamhuriyar Congo a ranar 8 ga watan Oktoba a Belgium.

Haka kuma za ta kara da Kamaru a wasan sada zumuntar ranar 11 ga watan Oktoba a filin wasa na Edmond Machtens.

Nigeria za ta karbi bakuncin Burkina Faso a filin wasa na Adokiye Amiesieamaka da ke Fatakwal a ranar 18 ga watan Oktoba a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Za kuma su fafata a karo na biyu a Ouagadougou ranar 25 ga watan Oktoban.