Enyeama ya yi ritaya daga bugawa Nigeria

Image caption Enyeama ne golan Nigeria a gasar cin kofin duniya

Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nigeria, Vincent Enyeama ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa kwallo bayan da kocinsa Sunday Oliseh ya cire shi daga mukamin kyaftin.

Enyeama, wanda ke taka leda a kungiyar Lille ta Faransa, shi ne wanda ya fi kowanne dan kwallo bugawa Nigeria inda ya buga sau 101.

Ya zama kyaftin ne bayan da Joseph Yobo ya yi ritaya bayan gasar cin kofin duniya a 2014.

"Ina son in godewa iyalai na da 'yan uwana da masu goyon baya da suka taimake ni cikin wannan shekara," in ji Enyeama.

Tuni Oliseh ya sanar da Ahmed Musa a matsayin kyaftin din Super Eagles wanda zai jagoranci tawagar a wasan sada zumunci da Congo da kuma Kamaru.

Enyeama ya soma bugawa Nigeria kwallo a watan Mayun 2002 a wasansu da Kenya.