Hayatou zai zama shugaban FIFA na riko

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Issa Hayatou

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce Issa Hayatou na kasar Kamaru zai zama mukaddashin shugabanta bayan an dakatar da Sepp Blatter na tsawon kwanaki 90.

A cikin wata sanarwa, hukumar FIFA ta ce Hayatou wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka zai zama mukaddashin shugabanta ne dai-dai da tsarinta na kasancewarsa wanda ya fi dadewa a matsayin mataimakin shugaba a kwamitin zartaswa.

Kwamitin da'a na hukumar FIFA ne ya dakatar da Blatter da wasu manyan jami'an hukumar guda biyu saboda zargin rashawa.

Issa Hayatou ya taba yin takarar neman shugabancin FIFA a shekarar 2002 inda ya sha kaye a hannun Sepp Blatter.