Mourinho ya gode wa Abramovich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce bai san dalilin da ya sa suka kasa taka rawar gani ba.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya nuna godiya ga mai kulob din Roman Abramovich saboda goyon bayansa duk da rashin taka rawar gani a kakar wasa ta bana.

Wata sanarwa daga Chelsea ta nuna goyon bayan ta ga Mourinho duk da yana cikin tsaka mai wuya.

Mourinho ya shaidawa mujallar Gazzetta cewar "Abramovich ya nuna kwarin gwiwarsa a kan manajan da ya lashe gasar Premier."

A cewar Mourinho, shi ma bai san abin da ya janyo wa Chelsea rashin taka rawar gani a kakar wasa ta bana ba.

Dan kasar Portugal din ya sabunta kwangilarsa a Stamford Bridge a watan Agusta.