U-17 Chile: Amuneke ya fitar da 'yan wasa 21

Image caption Za a fara gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 a Chile a ranar 17 ga watan Oktoba

Kocin tawagar matasa ta Nigeria, Emmanuel Amuneke ya fitar da sunayen 'yan wasa 21 da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya.

Chile ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 daga ranar 17 ga watan Oktoba zuwa 8 ga watan Nuwamba.

Nigeria ta samu tikitin shiga gasar ne bayan da ta kammala a mataki na hudu a wasan neman gurbin shiga gasar da aka yi a watan Fabrairu a Niger.

Nigeria ta lashe kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 na duniya a shekarar 1985 da 1993 da 2007 da kuma 2013.

Nigeria wacce take rukuni na daya za ta fara wasan farko da Amurka a ranar 17 ga watan Oktoba, sannan ta fafata da Chile a ranar 20 ga watan Oktoba ta kuma buga wasan karshe na cikin rukuni da Croatia ranar 23 ga watan nan da muke ciki.

Ga sunayen 'yan wasa 21 da Amuneke ya fitar:

Masu tsarar raga: Akpan Udoh, Chisom Chiaha, Amos Benjamin- Masu tsaron baya: John Lazarus, Lukman Zakari, Ejike Ikwu, Tobechukwu Ibe. Masu wasan tsakiya: David Enogela, Samuel Chukwueze, Kingsley Michael, Kelechi Nwakali, Chinedu Madueke, Chukwudi Agor, Joel Osikel, Edidiong Essien. Masu cin kwallo: Funsho Bamgboye, Victor Osimhen, Udochukwu Anumudu, Osinachi Ebere, Sunday Alimi, Orji Okwonkwo