Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

6:00 Wasu wasannin da za a buga ranar Lahadi 11 ga watan Oktoba.

Africa - Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya

 • 1:00 Malawi vs Tanzania
 • 2:00 Ethiopia vs São Tomé
 • 2:00 Kenya vs Mauritius

Turai - Wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

 • 5:00 Faroe Islands vs Romania
 • 5:00 Finland vs Northern Ireland
 • 5:00 Greece vs Hungary
 • 5:00 Armenia vs Albania
 • 5:00 Serbia vs Portugal
 • 7:45 Germany vs Georgia
 • 7:45 Gibraltar vs Scotland
 • 7:45 Poland vs Republic of Ireland

Wasannin sada zumunta

 • 5:00 Egypt vs Zambia
 • 7:45 Denmark vs France
 • 8:00 Nigeria vs Cameroon
Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter

5:45 Wasannin cin kofin firimiyar Nigeria mako na 33 da za a yi ranar Lahadi 11 ga watan Oktoba.

 • Giwa FC v Dolphins
 • FC Ifeanyiubah v El-Kanemi
 • Sharks v Wikki
 • FC Taraba v Heartland
 • Enyimba v Shooting Stars
 • Bayelsa Utd v Nasarawa Utd
 • Lobi Stars v Kwara Utd
 • Akwa Utd v Abia Warriors
 • Rangers v Wolves
 • Kano Pillars v Sunshine Stars
Hakkin mallakar hoto Getty

5:30 Shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini ya kalubalanci dakatar da shi da aka yi daga Fifa, bayan da ake yin bincike kan cin hanci. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

Hakkin mallakar hoto AP

5:18 Ya kamata ace an hukunta Hector Moreno a ketar da ya yi wa dan kwallon Manchester United, Luke Shaw in ji tsohon alkalin wasa Pierluigi Collina. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

5:15 Afirka - Sakamakon wasannin share fage na shiga karawar wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya

 • Central Africa… 0 - 3 Madagascar
 • Eritrea 0 - 2 Botswana
 • Chad 1 - 0 Sierra Leone
Hakkin mallakar hoto Reuters

4:52 Dan kwallon Bayern Munich, Mario Gotze zai yi jinyar watanni 10 zuwa 12 sakamakon raunin da ya ji in ji kungiyar.

Gotze mai shekaru 23 ya ji raunin ne a karawar da jamhuriyar Ireland ta ci Jamus daya mai ban haushi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a ranar Alhamis.

Dan wasan ba zai buga wa tawagar Jamus karawar da za ta yi da Georgia a ranar Lahadi, duk da Jamus na bukatar maki daya ta samu tikitin shiga gasar da Faransa za ta karbi bakunci a badi.

Haka kuma Gotze ba zai buga wa Bayern Munich wasanni biyu da za ta buga da Arsenal a gasar cin kocin zakarun Turai ba.

4:30 Wannan dambe ne da aka yi tsakanin Bahagon Sarka daga Kudu da kuma Cindo daga Arewa a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, kuma wannan takawar babu kisa.

Hakkin mallakar hoto Getty

4:22 Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta ce Issa Hayatou yana da koshin lafiya da zai iya aikin riko na shugaban Fifa, duk da rashin lafiya da yake fama da yi. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

3:30 Kocin tawagar matasa ta Nigeria, Emmanuel Amuneke ya fitar da sunayen 'yan wasa 21 da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

3:21 Kokawar gargajiya tana daga cikin wasannin Hausawa da suka dade suna gudanar wa.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:12 Samson Siasia ya gayyaci 'yan wasa 30 masu shekaru kasa da 23 zuwa sansanin horo a Abuja Nigeria. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

Cikin 'yan wasan ne zai fitar da wadanda za su wakilci Nigeria a gasar cin kofin nahiyar Afika ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 da Senegal za ta karbi bakunci a watan gobe.

2:25 Muhawar da kuke tafka wa a BBC Hausa Facebook

Sadi Energy Tandari Potiskum: Hakika daukan Jorgen Klopp da Liverpool ta yi za iya ciyar da kungiyar gaba har tagwamashinta ya dawo kamar da.

Imran Idris: Liverpool suna sayan 'yan wasa, amma bamanya ba ne su dunga sayen manyan suga aiki da cikawa. Up man united

Mohammed Al-barade Gombi: To Jurgen Klopp Premier fa ta wuce wasa domin wanda ya iyama sai ya yi da gaske kar a barka a baya, Up Yaya Toure

Usman Muhammad: Kloop kwararrene a fagen horas wa, kuma ya yi rawar gani a Dortmund inda ya taimaka musu wajen lashe Bundesliga, ina tunanin in har ya samu yan wasa masu hazaka zai dau Premier.

Hakkin mallakar hoto Getty

2:13 Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ya yi rauni a cinyarsa a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke Ecuador 2-0. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

1:38 Muhawar da kuke tafka wa a BBC Hausa Facebook

Boyes Saudiya: A yi dai mugani ai wannan bazai sa Liverpool sutabuka wani abun a zo a ganiba sun riga sun yi na su a baya, kuma kawo Klopp ba zai hana kananan kulob su zazzaga musu kwallo ba. 'up united for life.

Auwalun Dabai Unguwa Uku: Hakika Liverpool akwai matsaloli kamar na rashin saka kishi da zuciya a lokacin da su ke taka leda, tabbas Klopp ka iya sanya mu su kishi da zuciya domin tabbatar da samun nasarar Liverpool, sannan dole ne su ba shi dama ya kawo 'yan wasa wadanda yake gani za su kai kungiyar ga nasara, Klopp ka iya daukar musu gasar premier duba da yadda ya iya hada kungiya idan su ka ba shi hadin kai sosai.

Isah Isah Kwafsi Asarara Tab: Nima dai a gani na ba dauko Jorgen Klopp ba ne matsalar Liverpool. Babban dabbarwar da suke fuskanta ita ce rashin kishi a tsakanin 'yan wasan ta da Son kai.

1:22 Niger tana daf da samun damar kai wasannin shiga gasar cin kogin duniya, bayan da ta doke Somalia har gida da ci 2-0 a wasan share fage da suka yi a ranar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto Getty

Moussa Maazou ne ya ci wa Niger dukkan kwallayen bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Maazou wanda ke taka leda a Changchun Yatai ta China ya ci kwallon farko ne a minti na 58 sannan ya kara ta biyu a minti na 62.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

 • Somalia 0-2 Niger
 • Djibouti 0-6 Swaziland
 • The Gambia 1-1 Namibia

1:00 Turai - Sakamakon wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, Juma'a 09 ga watan Oktoba 2015.

 • Spain 4 - 0 Luxembourg
 • England 2 - 0 Estonia
 • Macedonia 0 - 2 Ukraine
 • Slovakia 0 - 1 Belarus
 • Slovenia 1 - 1 Lithuania
 • Switzerland 7 - 0 San Marino
 • Liechtenstein 0 - 2 Sweden
 • Moldova 1 - 2 Russia
 • Montenegro 2 - 3 Austria

12 56 Ingila ta lashe karawa tara da ta yi a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Estonia da ci 2-0 a ranar Juma'a a Wembley.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Walcott da Sterling ne suka ci wa Ingila kwallayen a karawar duk da Wayne Rooney bai buga wasan ba, sakamakon raunin da ya ji, kuma tuni ta samu tikitin shiga gasar da Faransa za ta karbi bakunci a badi.

Kafin a take kwallo Sir Bobby Charlton ya bai wa Rooney kwallon zinare, saboda kwallaye 50 da ya ci wa Ingila, kuma ya zura ta 50 dinne daga bugun fenariti da ya ci Switzerland a Wembley. Shi ne dan wasan da ya fi yawan ci wa Ingila kwallaye a raga a tarihi.

12:15 Gareth Bale zai buga wa Wales wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za ta yi da Bosnia-Herzegovina a ranar Asabar in ji kociya Chris Coleman.

Hakkin mallakar hoto PA

Bale ya ji rauni ne a cikin watan Satumba, amma ya yi wa Real Madrid kwallo a ranar Lahadi a gasar La Liga da ta tashi kunnen doki da Atletico Madrid.

Wales za ta iya samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a badi idan ta samu maki a Bosnia-Herzegovina ko kuma a karawar da za ta yi da Andorra nan da kwanki uku masu zuwa.

12:00 Afirka - Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya

 • 12:30 Central Africa vs Madagascar
 • 2:00 Eritrea vs Botswana
 • 3:30 Chad vs Sierra Leone

Turai - Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

 • 5:00 Iceland vs Latvia
 • 5:00 Kazakhstan vs Netherlands
 • 5:00 Azerbaijan vs Italy
 • 5:00 Norway vs Malta
 • 7:45 Czech Republic vs Turkey
 • 7:45 Andorra vs Belgium
 • 7:45 Bosnia-Herzegovina vs Wales
 • 7:45 Israel vs Cyprus
 • 7:45 Croatia vs Bulgaria