Novak Djokovic ya lashe gasar China Open

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Djokic shi ne na daya a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya

Wanda yake mataki na daya a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya Novak Djokovic ya lashe gasar China Open.

Djokovic ya lashe gasar ne, bayan da ya doke Rafael Nadal da ci 6-2 da kuma 6-2 a fafatawar da suka yi a China.

Wannan kuma shi ne karo na shida da Nadal ya buga wasan karshe a gasar kwallon tennis daban-daban da ya yi a shekarar 2015.

A karawar mata da aka buga wasan karshe a gasar, Garbine Muguruza ce ta dauki kofin bayan da ta doke Timea Bacsinszky.