"Za mu fara gudanar da gasar wasannin makafi"

Image caption Makafin na son a dinga damawa da su a wasanni

Shugaban kungiyar makafi ta Nigeria, Isyaku Adamu Gombe ya ce za a fara gudanar da gasar wasannin makafi ta kasa a shekara mai zuwa.

Shugaban ya ce tun lokacin da ya karbi ragamar kungiyar a watan Janairu ya ware sashe da yake kula da farfado da wasannin makafi.

Ya kuma ce cikin kokarin da suke na ganin ana damawa da makafi a wasanni a fadin Nigeria da duniya, sun tuntubi hukumar wasannin Olympics ta Nigeria za kuma su nemi tattaunawa da hukumar da ke kula da wasannin makafi ta duniya da ke Faransa.

Isyaku ya kara da cewar tuni guragu suka yi nisa wajen wakiltar Nigeria a wasannin kwallon guragu, saboda haka bai ga dalilin da makafi ma ba za su wakilci kasar a nan gaba ba.

Cikin wasannin da makafin za su fafata sun hada da kwallon kafa da daga nauyi da linkaya da kuma guje-guje da sauransu.