Depay da Van Persie sun yi cacar baki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Holland ce ta doke Kazakhstan da ci 2-1 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

Dan wasan Manchester United, Memphis Depay, da kuma Robin van Persie na Fenerbahce sun yi cacar baki a wurin atisayen tawagar kwallon kafar Netherlands.

Kociyan Holland Danny Blind ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya faru kafin buga wasan da suka doke Kazakhstan 2-1 a ranar Asabar, amma ya karyata cewar abin ya yi tsanani.

Kocin ya kuma ce kin saka van Persie a cikin 'yan wasa 11 da suka fara wasa da Kazakhstan bai shafi sa-in-sar da ya yi da Depay ba.

Van Persie shi ne dan wasan Holland da ya fi ci wa tawagar kwallaye, a inda ya ci 49 daga wasanni 100 da ya buga mata, kuma na darinne wanda ya yi a ranar Asabar a inda ya canji wani dan wasan.