Tim Krul zai yi jinya mai tsawo

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Newcastle United ba ta ci wasa ba tun fara gasar Premier bana

Mai tsaron ragar Newcastle United, Tim Krul, ba zai ci gaba da buga wasannin kwallon kafar bana ba, sakamakon raunin da ya ji.

Krul ya ji rauni ne a gwiwarsa lokacin da yake yi wa Netherlands wasa a karawar da ta doke Kazakhstan da ci 2-1 a ranar Asabar.

Dan kwallon mai shekaru 27, zai koma Newcastle domin kungiyar ta kara auna girman raunin da ya ji.

Krul shi ne Golan Newcastle da ya buga mata dukkan wasanni takwas da ta fafata a Premier bana, wacce ke mataki na karshe a kan teburin gasar.

Tuni kuma kungiyar ta maido da mai tsaron ragarta Freddie Woodman, wanda ta bayar aro ga Crawley Town domin ya zauna a matsayin kar-ta-kwana.