'Yan sanda sun sako Djibril Cisse

Djibril Cisse Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kama Djibril Cisse ne bisa zaton yana da hannu a bata sunan wani dan wasa

'Yan sandan Faransa sun sako tsohon mai buga wasan gaba a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Djibril Cisse, wanda aka kama a wani bangare na binciken da ake kan zargin bata sunan wani dan kwallo.

Cisse na cikin mutanen da aka tsare a ranar Talata a Versailles bisa wani bincike da aka fara tun a watan Yuli.

Sai dai masu shigar da kara sun ce ba a zaton Cisse na da hannu a lamarin.

'Yan sanda sun ce batun bata sunan ya jibinci wadansu hotunan batsa da aka dauka a wayar salula. Idan aka samu mutum da irin wannan laifin, zai iya shan daurin shekaru biyar a kurkuku.