Andy Murray ya yi nasara a Shanghai

Andy Murray Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray ya ce ya yi wasa sosai, kuma ya fara da kafar dama

Dan wasan tennis na biyu a duniya, Andy Murray, ya yi nasara a kan Ba'amerike Steve Johnson a wasanshi na farko a Gasar Shanghai Masters.

Dan Burtaniyar ya kifar da damarsa a turmi na farko, amma Johnson bai daga masa hankali ba a wasan, wanda shi ne na farko da ya buga tun bayan nasarar da ya yi a wasan daf da na karshe na Gasar cin Kofin Davis ta Burtaniya.

A zagaye na uku na Gasar, Murray zai kara ne da wani Ba'amurken ne, John Isner, wanda a game da shi ya ce:

"Ya taka rawar gani sosai bana, kuma ya nuna jajircewa fiye da a baya, saboda haka karawar za ta yi zafi".

Karin bayani