Ka da a dage zaben Fifa —Yarima Ali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yarima Ali bin Hussein na cikin 'yan takarar shugabancin maye gurbin tsohon shugaban FIFA, Sepp Blatter.

Daya daga cikin masu takarar shugabancin Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Yarima Ali bin al-Hussein ya ce bata lokaci wurin maye gurbin Sepp Blatter zai janyo matsala.

Hussein, wanda dan asalin kasar Jordan ne, yana cikin masu takarar zaben da zai maye gurbin tsohon shugaban da aka dakatar, Sepp Blatter, wanda za a gudanar a watan Fabrairun badi.

Ana zaton za'a dage zaben bayan dakatar da shugaban FIFA Sepp Blatter mai shekaru 79, da shugaban hukumar kwallon kafa na Turai UEFA, Michel Platini mai shekaru 60, da aka yi.

Yarima Ali ya ce gudanar da zaben zai nuna wa duniya cewa an dauki darasi a kan lamarin da ya auku.

Dan asalin kasar Switzerland, Sepp Blatter da bafaranshe Michel Platini sun kalubalance dakatarwar da aka yi masu na kwanaki 90.

Shi ma sakatare janar na Fifa, Jerome Valcke an dakatar da shi sai dai dukkanin su uku sun musanta aikata ba daidai ba.