FA ta ci tarar Jose Mourinho £50,000

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho ya ce FA ba ta hukunta sauran masu horar da 'yan wasa

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ta ci tarar kocin Chelsea, Jose Mourinho, £50,000, sannan ta haramta halartar wasa guda, saboda wadansu kalamai da ya furta game da jami'an wasa.

Mourinho dai ya yi ikirari ne cewa tsoro ne ya hana jami'an bai wa 'yan wasanshi bugun fanareti bayan da alkalin wasa Robert Madley ya ya hana Chelsea bugun tazara a wasan da suka buga da Southampton wanda suka sha kashi da ci 3-1.

A cewar hukumar ta FA, kalaman Mourinho na nuni da cewa alkalan wasan sun yi son-kai.

Sai dai kuma za a aiwatar da haramcin da aka yi wa Mourinho ne kawai idan ya sake aikata laifin a cikin shekara guda mai zuwa.

Wasan, wanda Southampton ta bi Chelsea har gida ta fi ta rawa, shi ne na hudu da kungiyar ta Chelsea ta sha kashi a wasannin takwas din ta buga a farkon kakar wasanni ta bana.