Ronaldo ya lashe kyautar takalmin zinare

Image caption Ronaldo na ci gaba da haskakawa

Cristiano Ronaldo ya ce yana sa ran yin ritaya a Real Madrid bayan da ya lashe kyautar takalmin zinare a karo na hudu.

Dan kasar Portugal din ya zura kwallaye 48 a cikin wasannin gasar La Liga 35 inda ya shiga gaban Lionel Messi na Barcelona.

"Buri na shi ne in yi ritaya a Real Madrid," in ji Ronaldo.

Ya kara da cewar "Idan mutum yana lura da kansa zai iya kai wa shekaru 40 yana murza leda."

Dan shekaru 30 ya koma Real ne a shekarar 2009 daga Manchester United kuma a yanzu babu dan kwallon da ya kai shi zura kwallo a Bernabeu.