UEFA ta tuhumi Ingila da Lithuania

Michel Platini Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban UEFA, Michel Platini

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA, ta tuhumi hukumomin kwallon kafa na Ingila da Lithuania game da tashin-tashinar da ta biyo bayan wasan da suka buga a Vilnius ranar Litinin na neman gurbi a Gasar cin Kofin Nahiyar Turai ta 2016.

'Yan sandan kwantar da tarzoma ne suka shawo kan yamutsin da ya barke a tsakanin magoya bayan tawagogin biyu ana daf da fara wasan, wanda Ingila ta lashe da ci 3-0.

Wata sanarwa da Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta fitar ta ce ba a wurin da magoya bayan da suka sayi tikita a wurinta rikicin ya barke ba.

Ranar 22 ga watan Oktoba za a saurari bahasi a kan batun.

Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta bukaci hukumomi su zakulo duk wani wanda ke da hannu a lamarin su kuma hukunta shi yadda ya kamata.

Karin bayani