'Ya kamata 'yan Liverpool su nuna jaruntaka'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klopp zai fuskanci kalubale a Liverpool

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce yanason ya ga 'yan wasansa na kara "jaruntaka", a yayin da yake shirin jagorantar tawagar a wasansa na farko.

Dan kasar Jamus din mai shekaru 48, a makon da ya gabata ne ya maye gurbin Brendan Rodgers.

A yanzu Liverpool ce ta 10 a kan teburin gasar Premier, kuma za ta fuskanci Tottenham a ranar Asabar.

Klopp ya ce "Ina son 'yan wasa na su bude kirji, su yi gudu, su kuma fafata."

Tsohon kocin Borussia Dortmund din ya bayyana jan ragamar Liverpool a matsayin aiki mafi kalubale a duniya.