Tennis: Murray ya doke Isner a Shanghai Masters

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andu Murray

Andy Murray ya samu kai wa zagayen gab da na kusa da karshe a gasar Tennis ta Shanghai Masters bayan ya doke John Isner.

Dan Burtaniyan kuma na biyu a duniya mai shekaru 28, ya nuna jumuri sosai dangane da matsin da ya fuskanta daga wurin Ba'amurken inda suka tashi da ci 6-7 da 6-4 da kuma 6-4.

Murray zai kara da Tomas Berdych ko Gilles Simon a karawarsa ta takwas ranar Juma'a.

Ya ce "karawa da Isner ba dadi a ko wanne lokaci, kafin wasa yazo zan ji kamar komai na hannuna, amma idan aka hadu sai a gane ba dadi".

Murray ya kara da cewa dan wasa yana gwada hakurin da yake da shi ne a lokacin da yake karawa da Isner.

Wannan shi ne karo na biyar da Murray ke samun nasara a fafatawar da ya yi da Isner a gasar.