Pistorius zai koma daurin talala

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Oscar Pistorius

Dan tseren nan na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius da a ka daure a kurkuku saboda kashe budurwarsa, zai koma zaman daurin talala a gidansa daga ranar Talata.

A bara ne aka yanke wa Pistorius daurin shekaru 5 a gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin kisan kai ko kisa ba da gangan ba.

Dan tseren ya harbe Reeva Steenkamp ne ta kofar bandaki da take rufe, inda ya ce yayi zaton barawo ne ya shigan masa gida.

Pistorius ya shafe watanni 12 a gidan yari amma yanzu zai karasa sauran wa'adin a matsayin daurin talala.

A cikin watan Augusta, Ministan Shari'a na kasar Afirka ta Kudu Michael Masutha ya ki amince wa da wata shawara da ke neman a saki Pistorius gaba daya.