Martial ya lashe kyautar watan Satumba

Hakkin mallakar hoto PA

Dan kwallon Manchester United Anthony Martial, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon gasar Premier na watan Satumba.

Dan wasan mai shekaru 19, ya zura kwallaye uku cikin wasanni hudu a watan da ya wuce.

Martial shi ne dan wasa mafi tsada mai kankantar shekaru a duniya, inda aka siyo shi daga Monaco a kan fan miliyan 36.

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino shi ne ya lashe kyautar a bangaren masu horadda 'yan kwallo.

Cikin nasararsa hadda wasan da suka doke Man City da ci hudu da daya a White Hart Lane.