Mourinho zai kalubalanci matakin FA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho na tsaka mai wuya

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce zai kalubalanci tarar fan dubu 50 da hukumar kwallon Ingila ta yi masa.

Dan kasar Portugal din ya bayyana tarar a matsayin "abin kunya".

Mourinho ya ce alkalan wasa na fargabar bada bugun fenariti, bayan da alkalin wasa Robert Madley ya ki bai wa Chelsea fenariti a wasan da Southampton ta doke su da ci uku da daya.

A ranar Laraba aka bayyana cewar idan har Mourinho ya kara irin wadannan kalaman, za a dakatar da shi na wasa guda.

Sai dai hukumar FA din ba za ta dauki wani karin hukunci ba a kan Mourinho ba.

A yanzu dai Chelsea ce ta 16 a kan teburin gasar Premier inda aka buga wasanni takwas.