Bayern Munich ta lashe wasanni 9 a jere

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ta kafa tarihin lashe wasanni tara a jere a gasar Bundesliga

Bayern Munich ta zama kungiya ta farko da ta lashe wasanni tara a jere a gasar Bundesliga, bayan da ta ci Werder Bremen daya mai ban haushi.

Munich din ta kafa wannan tarihin ne bayan da ta ziyarci Werder Bremen a gasar Bundesliga wasan mako na tara da suka fafata a ranar Asabar.

Thomas Muller ne ya ci wa Munich kwallon a minti na 23, bayan da ya samu tamaula daga wajen Thiago ya kuma zura ta a raga.

Haka kuma wannan ne wasan farko da Robert Lewandowski bai ci kwallo ba a wasanni bakwai da ya yi, bayan da ya ci kwallaye 15 a wasanni shida da ya yi wa Bayern da Poland.

Werder Bremen ta samu damar farke kwallon da aka zura mata ta hannun Anthony Ujah, amma golan Munich, Manuel Neuer ya hana ta shiga raga.

Bayern ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Bundesliga, yayin da Werder Bremen ke matsayi na 14 a gasar.