'Za mu dauki Premier idan muka doke Man City'

Hakkin mallakar hoto
Image caption United tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 19

Louis van Gaal ya ce da zarar Manchester United ta doke Manchester City a gasar Premier da za su yi a ranar Lahadi, suna daga cikin wadanda za su iya lashe kofin bana.

United din ta doke Everton da ci 3-0 a Goodison Park a ranar Asabar, yayin da Manchester City ta lallasa Bournemuth da ci 5-1 a Ettihad.

Morgan Schneiderlin da Ander Herrera da kuma Wayne Rooney ne suka ci wa United kwallaye ukun a karawar.

Van Gaal ya ce harin da suke yi shi ne su zama zakaru, kuma abu ne mai mahimmaci da suke son cimma.

Ya kuma kara da cewar ya ji dadi da yadda 'yan wasa suka murza leda da kwazon da suka yi, yana mai alfahari da su.

Kocin ya kuma kara da cewar ya kamata su dora a kan kokarin da suke yi, "Kuma da zazar mun doke City a wasan gaba, zan gamsu da cewar za mu iya lashe kofin Premier bana", in ji shi