Novak Djokovic ya lashe Shanghai Masters

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Novac ya lashe gasa tara a wasannin shekarar bana

Novak Djokovic ya lashe gasar kwallon tennis ta Shanghai Masters, bayan da ya samu nasara a kan Jo-Wilfried Tsonga.

Djokovc dan kasar Serbia ya samu nasara ne a kan Jo-Wilfried Tsonga dan kasar Faransa da ci 6-2 da kuma 6-4 a cikin mintina 78 da suka kara a filin wasa na Qi Zhong.

Wannan ita ce gasa ta tara da ya lashe a kakar bana, ciki har da Grand Slam uku daga ciki hudu da ya dauka.

Hakan kuma ya sa ya dauki kofin kwararru da ake kira masters guda 25, ya dara Roger Federer da kofi daya sannan saura biyu ya kamo Rafael Nadal na Spaniya.