Ronaldo ne kan gaba wajen ci wa Madrid kwallaye

Image caption Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 18

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan Real Madrid da ya fi ci mata kwallaye a raga, bayan da ya zura daya a karawar da suka doke Levente 3-0 a wasan La Liga a ranar Asabar.

Hakan ne ya sa Ronaldo mai shekaru 30, ya ci kwallo ta 324 daga wasanni 310 da ya yi wa Real Madrid, sannan ya kuma dara Raul wanda ke rike da tarihin a baya.

Raul wanda ke taka leda a New York Cosmos ta Amurka wanda zai yi ritaya daga buga tamaula a watan Nuwamba, ya ci wa Real Madrid kwallaye 323 daga wasanni 741 da ya yi mata.

Sai dai kuma ana ci gaba da takaddama a kwallon da ta doki Pepe da Ronaldo ya buga ta shiga raga a shekarar 2010, a inda Madrid ta bai wa Ronaldo.

Masu gudanar da gasar La Liga cewa suka yi Pepe ne ya ci kwallon, ita kuwa Madrid cewa ta yi Ronaldo ne ya yi sanadiyyar kwallon da ta fada ragar.