Arewa Sun fi Kudu yawan kisa a damben lahadi

Image caption Shagon Alhazai da Autan Faya, wannan takawar babu kisa a tsakaninsu

Damben da aka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Deai a Abuja Nigeria, Arewa ne suka fi yin kasa a kan Kudawa.

Takawar Farko Shagon Shagon Lawwali daga Arewa ne ya kashe Shagon Shagon Mada daga Kudu.

Sa zare a wasa na biyu Shagon Buzu ne daga Arewa ya buge Autan Bahagon Babangida daga Kudu, sai kuma Bahagon Soja daga Arewa da shi kuma ya buge Abbati daga Kudu.

Damben Autan Faya daga Kudu da Shagon Alhazai daga Arewa babu kisa, shi ma wasan Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa da Garkuwan Dan Digiri daga Kudu babu wanda ya je kasa.

Fafatawa tsakanin Audu Na Mai Kashi daga Kudu da Nokiyar Dogon Sani daga Arewa ma ba a yi kisa ba, dambatawa da aka yi tsakanin Nura na Dogon Sani daga Arewa da Garguwan Dan Digiri daga Kudu an biya 'yan kallo sai dai babu kisa a karawar da suka yi turmi uku.

Daga karshe ne aka rufe wasan lahadi da safe tsakanin Bahagon Dakakin Dakaka daga Kudu da Shagon Bahagon Musa daga Arewa kuma turmi biyu suka yi aka raba wasan.